Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har yanzu Najeriya ba ta kai kololuwar yawan adadin masu harbuwa da COVID-19 ba
2020-06-02 20:00:44        cri

Shugaban kwamitin ko ta kwana na fadar shugaban tarayyar Najeriya game da yaki da cutar COVID-19, kuma sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha, ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai kololuwar yawan adadin masu harbuwa da cutar numfashi ta COVID-19 ba.

Shugaban kwamitin na PTF, ya shaidawa manema labarai hakan a jiya Litinin, yana mai cewa yaki da wannan cuta, aiki ne da za a shafe tsawon lokaci ana fama da shi.

Boss Mustapha, ya ce mafi yawan masu harbuwa da wannan cuta na zaune ne a wasu kananan hukumomin kasar 'yan kadan, duba da cewa kananan hukumomin kasar 20 cikin jimillar 774 dake Najeriyar ne ke dauke da kaso 60 bisa dari, na masu fama da cutar.

Jami'in ya kara da cewa, kwamitin PTF ya shawarci shugaban kasar Muhammadu Buhari, da ya baiwa gwamnatin jihohin kasar damar aiwatar da matakan sassauta dokar kulle a jihohin su, ciki hadda batun sake bude makarantu, da kasuwanni da wuraren bauta, wadanda aka rufe tun cikin watan Maris, a matsayin mataki na kokarin dakile annobar COVID-19.

Gwamnatin Najeriyar dai ta nuna damuwar ta game da yawaitar karuwar masu harbuwa da wannan cuta a sassan kasar, a gabar da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar ta fitar da alkaluma, dake nuna karuwar sabbin mutane 416 da cutar ta harba a daren jiya Litinin.

Da wannan sabbin alkaluma, yawan wadanda suka harbu da COVID-19 a kasar ya kai mutum 10,578, ciki hadda 299 da suka rasu, da kuma 3,122 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China