Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gogewar Sin a fannin yaki da talauci ya ja hankali sosai a Afrika
2020-10-17 15:29:06        cri

Cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, kasar Sin ta rage adadin matalauta a kasar da miliyan 850, wanda ya dauki kaso 70 cikin dari, na yawan wadanda aka fitar daga talauci a duniya. Gogewar kasar Sin a fannin rage talauci, abu ne da ya ja hankalin mutane sosai a nahiyar Afrika, wadda ke da adadi mafi yawa na kasashe masu tasowa.

A bara, Nijeriya wadda ta fi ko wace kasa yawan al'umma a nahiyar, ta gabatar da wani shiri na fitar da mutane miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10 masu zuwa.

Wani babban mai nazari a cibiyar nazarin harkokin waje ta Nijeriyar, Efem Ubi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, gogewar kasar Sin a wannan fanni zai yi matukar amfani ga Nijeriya, musammam la'akari da cewa, dukkansu kasashe ne dake da yawan al'umma. Ya yi imanin cewa, ya kamata kasashen Afrika su yi koyi da kasar Sin wajen samar da dabarun da suka dace da yanayi da halayyarsu a yankunan masu fama da talauci.

Shi kuwa ministan kula da kananan hukumomi da ayyukan gwamnati da samar da gidaje na kasar Zimbabwe, July Moyo, cewa ya yi, nasarar da Sin ta samu wajen yaki da talauci ya samarwa Zimbabwe darasi mai daraja, kuma zai taimaka mata wajen cimma burinta na zama kasa mai matsakaicin kudin shiga zuwa shekarar 2030 kamar yadda aka tsara.

Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin, tana iya ware albarkatu yadda ya kamata, sannan ta tattara tare da hada kan dukkan al'umma, ta kuma fitar da su daga kangin talauci ta hanyar aiwatar da tsauraran matakai daki-daki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China