2020-07-23 10:46:03 cri |
Mr. Korankye-Sakyi, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce karkashin dadadden tsarin hadin gwiwar ta da Afirka, Sin ta taka rawar gani, wajen ingiza cimma nasarar ajandar nahiyar ta nan da shekarar 2063, kudurin da shi ne ya haifar da yarjejeniyar ta AfCFTA.
Korankye-Sakyi, wanda kuma shi ne babban jami'in ofishin Afirka na tsara manufofin zuba jari a kasar Ghana, ya kara da cewa, Sin ta saukaka cudanyar ta da Afirka, ta hanyar goyawa nahiyar baya, da samar mata da hidimomi bisa tsari da bin doka. Ta kuma samar da kudaden gudanar da muhimman ayyuka ba tare da gindaya irin sharuddan da kasashen yamma ke sanyawa kasashen nahiyar ba.
A nasa tsokaci, shugaban kamfanin fasaha na mPedigree dake birnin Accra Mr. Bright Simons, ya yi hasashen cewa, saurin kafa kyakkyawar alakar tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka, ya baiwa Sin din damar bunkasa hada hadar cinikayya da nahiyar, sama da sauran abokan takarar ta karkashin sabuwar yarjejeniyar ta AfCFTA. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China