Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin CPC sun nazarci taswirar yankin tattalin arziki na Chengdu-Chongqing
2020-10-16 20:50:40        cri

A yau ne hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS ta yi wata ganawa, don bitar babbar taswirar yankin tattalin arziki na Chengdu-Chongqing da ake fatan ginawa.

Taron wanda babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping ya jagoranta, ya yi nuni da cewa, gina yankin tattalin arzikin, wani muhimmin mataki ne, a kokarin da ake na samar da sabon ci gaba da zai dace da kasuwannin cikin gida, da ma baiwa kasuwannin cikin gida da na ketare damar raya kansu.

Bugu da kari, taron ya jaddda cewa, za a yi kokarin inganta yankin na Chengdu-Chongqing, dake yankin kudu maso yammacin kasar Sin, zuwa wata muhimmiyar cibiyar tattalin arziki, cibiyar kimiya da fasahar kirkire-kirkire, wata sabuwar kafar bude kofa da yin gyare-gyare, wurin da za a dogara da shi a fannin rayuwa mai inganci, kana muhimmin wuri ga kokarin kasar na samun ci gaba mai inganci.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China