2020-10-15 19:51:01 cri |
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, kasarsa tana adawa da ma Allah wadai da dokar 'yancin gashin kai da Amurka ta bijiro da ita kan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, da shawarar da ta yanke ta kakabawa wasu mutane takunkumi. A don haka kasar Sin, ta bayyana rashin jin dadinta ga Amurkar kan matakinta na kakabawa jami'anta takunkumi.
Zhao ya jaddada cewa, idan har Amurka ta nace kan daukar wannan mataki maras dacewa, babu shakka kasar Sin za ta mayar da martanin da ya dace, don kare 'yanci da muradunta na tsaro da 'yanci da muradun kamfanoni da jami'anta.
Jiya ne dai, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka, ta gargadi hukumomin kudi na kasa da kasa cewa, muddin suka gudanar da harkokin kasuwanci da mutanen da wannan batu ya shafa a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, ciki har da jagorar yankin Carrie Lam, to za su fuskanci takunkumi mai tsanani ba tare da bata lokaci ba.
Don haka, kasar Sin ta bukaci Amurka, da ta gyara kuskurenta, ta kuma daina tsoma baki a harkokin cikin gidanta ta ko wace hanya.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China