Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan jakadan Amurka dake Sin zai ci gaba da taka kyakkyawar rawa bayan kammala aiki
2020-09-18 20:39:33        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan jakadan Amurka dake kasar Sin Terry Branstad, zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa alaka mai kyau tsakanin kasashen biyu, bayan ya kammala aikinsa.

Wang wanda ya bayyana haka yayin taron manema labaran da aka shirya Jumma'ar nan, ya ce Branstad ya yi kokari matuka, wajen bunkasa musaya da hadin gwiwa tsakanin al'ummomin kasashen biyu, a lokacin da yake rika da mukamin gwamnan jihar Iowa da kuma jakadan kasar Amurka a Sin.

A lokatu da dama dai, wasu 'yan siyasar Amurka, sun sha yin ikirarin cewa, kasar Sin ta samu ci gabanta ne ta hanyar satar fasahohin sauran kasashe da ma ci da gumin wasu. Sai dai jami'in na kasar Sin, ya nanata cewa, wannan zargi ne kawai, saboda cimma wata manufa ta daban. Yana mai cewa, kasashe duniya da ma wadanda suka fahimci gaskiyar al'amura a kasar ta Amurka, sun san gaskiya kan wannan batu.

A nasa jawabin, jakada Branstad, ya ce, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a 'yan gomman shekarun da suka gabata. Yana mai cewa, yadda Sinawa ke aiki tukuru, da sadaukar da kai ga harkar ilimi, da iyali da sana'a, sun taimaka ga ci gaban kasar.

A ranar Litinin din da ta gabata ce, kasar Amurka ta sanarwa kasar Sin a hukumance cewa, jakada Branstad zai kammala aikinsa a farkon watan Oktoba wannan shekara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China