Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar numfashi ta COVID-19 ta sake barkewa a wasu kasashe
2020-10-15 11:29:15        cri
Hukumar lafiyar duniya ta WHO ta fidda sabon rahoto dake cewa, daga farkon wannan wata na Oktoba, sau da dama, adadin masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 cikin yini guda a kasashe daban daban, ya zarce adadi na da. Kuma kasashe da dama, sun sanar da shiga sabon lokaci na barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a karo na biyu.

A karshen watan Satumba, firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya sanar da cewa, kasarsa ta shiga lokacin barkewar cutar COVID-19 karo na biyu, yana mai gargadin cewa, mai yiyuwa ne, a wannan karo, yanayin yaduwar cutar zai fi karo na farko tsanani.

Haka kuma, shugaban cibiyar kula da harkokin gaggawa a ma'aikatar harkokin kiwon lafiyar kasar Sifaniya Fernando Simon, ya gaskata cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta sake barkewa a kasarsa.

Bugu da kari, firaministan kasar Faransa Jean Castex, ya bayyana a ranar 12 ga wata cewa, cutar numfashi ta COVID-19 ta sake barkewa a kasar Faransa.

Dangane da wannan lamari, jami'i mai kula da harkokin gaggawa na hukumar WHO Michael Ryan ya bayyana cewa, matukar karuwar adadin masu kamu da cutar, ba ya nufin barkewar cutar a karo na biyu, mai yiyuwa ne hakan ya zama wani ci gaba ne na barkewar cutar COVID-19 a karo na farko. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China