Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta yabawa Sin game da sakamakon da ta cimma na dakile yaduwar cutar COVID-19
2020-09-09 11:13:00        cri
Wasu jami'an hukumar kiwon lafiyar duniya wato WHO sun nuna yabo matuka game da nasarar da kasar Sin ta cimma wajen dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19.

Jami'an sun bayyana yayin taron manema labarai da aka shirya a birnin Geneva ranar Litinin da ta gabata cewa, fasahohin kasar Sin sun taimakawa duniya matuka wajen dakile yaduwar annobar

Mashawarcin babban sakataren hukumar WHO Bruce Alyward ya takaita dalilai guda uku, wadanda suka sa kasar Sin ta cimma nasarar yaki da cutar. Ya ce, na farko, Sin ta zuba jari masu dimbin yawa don gina ababen more rayuwa a fannin kiwon lafiya. Haka kuma, dukkanin al'ummomin kasar Sin sun ba da hadin kai yadda ya kamata. A karshe ya ce, kasar Sin tana ci gaba da karfafa matakan dakile yaduwar annoba, ko da yake, adadin masu kamuwa da cutar a kasar yana ci gaba da raguwa.

A nata bangare, shugabar kula da harkokin gaggawa ta hukumar WHO Maria Van Kerkhove ta ce, kasar Sin tana da kayayyakin kiwon lafiya masu inganci, da tsarin binciken yanayin yaduwar cutar COVID-19 mai kyau, da kuma kwararrun ma'aikata a fannin yaki da cutar. Haka kuma, ta ce, a halin yanzu, akwai kasashe da dama da suke koyon fasahohin kasar Sin wajen yaki da cutar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China