Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya: Matalautan kasashe suna tsananin bukatar tallafi don farfadowa
2020-10-15 11:09:49        cri

Tattalin arzikin duniya yana fuskantar matsin lamba wajen farfadowa, yayin da kasashe masu arziki suke da sukunin samar da tallafin fardowa amma kasashe matalauta suna ci gaba da fuskantar matsanancin karayar tattalin arziki, shugaban kamfanin bankin duniya David Malpass shi ne ya bayyana hakan.

Malpass ya bayyana a taron manema labarai ta kafar bidiyo a yayin taron kamfanin bankin duniya da asusun bada lamini na duniya wato IMF cewa, abin da ake gani a halin yanzu shi ne, wani abu ne da za a bayyana da sigar farfadowar tattalin arziki ta "K-shaped recovery".

A cewar Malpass, abin da hakan ke nufi shi ne, kasashe mafiya karfin tattalin arziki suna iya samarwa al'ummarsu tallafi, musamman a fannin kasuwannin hada hadar kudi da kuma mutanen da suke da ayyuka wadanda za su iya yin aiki daga gida.

Amma ga kasashe masu tasowa, musamman matalautan kasashe wadanda aka musu lakabi da harafin K, mutane suna matukar fuskantar koma bayan tattalin arziki, saboda sun rasa ayyukansu, sun rasa hanyoyin samun kudin shigarsu, kana sun rasa kudade daga ma'aikatan dake ayyuka a kasashen waje. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China