Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na maraba da karin gyare-gyare da ci gaba a yankunan musammam na raya tattalin arziki
2020-10-14 13:12:33        cri
Yayin bikin cika shekaru 40 da kafuwar Shenzhen, a matsayin yankin musammam na raya tattalin arziki a yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, da badan wasu kasashe sun shiga an dama da su ba, da yankunan musammam na raya tatalin arziki na kasar ba su samu irin ci gaban da suka samu cikin shekaru 40 da suka gabata ba, lamarin da ya ce, ya fadada damarsu na samun ci gaba da musayar muradunsu na raya kai. Shugaba Xi ya kara da cewa, Sin na maraba da karin kasashe su shiga a dama da su cikin manufarta ta gyare-gyare da bude kofa da raya yankunanta na musammam domin samar da wani sabon tsarin zurfafa tuntubar juna da hada hannu wajen bada gudunmuwa da kuma samun moriya tare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China