Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya ziyarci birnin Shantou dake kudancin kasar
2020-10-14 10:14:42        cri

Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, ya ziyarci a birnin Shantou jiya Talata, a wani bangare na rangadinsa a lardin Guandong dake kudancin kasar.

Yayin da yake rangadi a Shantou dake da tarihin manufar bude kofa ta kasar Sin, shugaba Xi ya ziyarci dakin nune-nune da na adana kayakin tarihi na Sinawa mazauna kasashen ketare, domin fahimtar tarihin birnin na bude kofa a matsayin tashar jirgin ruwa da ci gaban da ya samu a matsayin yankin raya tattalin arziki na musammam da kuma tarihin Sinawa mazauna ketare 'yan asalin birnin na Shantou da Chaozhou da yankuna makwabta, dake kulawa tare da goyon bayan gina mahaifarsu da ma kasarsu baki daya.

Daga bisani, shugaban ya zagaya tsoffin titunan wasu yankuna tare da tattaunawa da mazauna wuraren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China