Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Za Mu Ci Gaba Da Dukufa Wajen Raya Yankin Tattalin Arziki Na Musamman
2020-10-14 12:55:55        cri

Yau Laraba, an yi bikin taya murnar cika shekaru 40 da kafuwar yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen na kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da muhimmin jawabi a yayin bikin, inda ya ce, "za mu ci gaba da raya yankin tattalin arziki na musamman zuwa wani sabon matsayi, da kuma kyautata harkokin da suka shafi yankin bisa dukkanin fannoni.

Ya ce, "ya kamata birnin Shenzhen ya tsaya tsayin daka kan sabbin ra'ayoyin neman bunkasuwa, domin samun dauwamammen ci gaba mai inganci, mai adalci, maras hadari kuma cikin sauri."

Ya kara da cewa, "Yanzu, mun shiga sabon lokaci na yin kwaskwarima, ya kamata kuma mu tsara dabaru da idon basira, domin zurfafa aikin kwaskwarima a muhimman fannnoni. Ya kuma jaddada cewa, burin al'ummar kasar Sin na samun zaman rayuwa mai dadi, shi ne babban burin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, don haka ya kamata a gudanar da ayyukan kwaskwarima a yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen, domin cimma wannan buri.

Birnin Shenzhen zai kasance abun misali ta fuskar kasancewar sa yankin musamman da aka gina bisa tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin. Kuma a nan gaba, za a inganta aikin ginawa babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao na GBA, domin tsara wasu sabbin hanyoyin raya yankunan kasa bisa tsarin "kasa daya, tsarin mulki iri biyu". (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China