2020-10-14 11:51:33 cri |
Yayin taron karawa juna sani da aka shirya a Larabar nan, albarkacin bikin murnar cikar birnin Shenzhen shekaru 40 da zama yankin tattalin arziki na musamman, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce an shirya zaman na yau ne domin bitar kwarewar da Sin ta samu, wajen kafa yankunan musamman na raya tattalin arziki, tare da sake ingiza sauye-sauye, da bude kofa ga waje daga sabon mafari.
Shugaba Xi ya ce, Shenzhen na daya daga cikin yankunan musamman na farko-farko da Sin ta kafa. Kuma a kusan shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen ya kafa muhimmin tarihi na bunkasa, daga karamin kauye dake kan iyaka zuwa birni mai matukar tasiri a mataki na kasa da kasa.
Cikin jawabin nasa, Xi ya ce birane masu karsashi, na nunawa duniya karfin kasar Sin a fannin aiwatar da sauye-sauye, da bude kofa ga waje, da ma kyakkyawar makomar da salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman da Sin ke da shi. (Saminu Alhassan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China