Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam mai daukar hoto
2020-10-12 09:59:45        cri

Kasar Sin ta yi nasarar harba sabon tauraron dan Adam mai daukar hoto, wanda kuma ake iya sarrafawa da na'ura wato remote, daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Xichang dake kudu maso yammacin kasar Sin, da misalin karfe 12:57 jiya daddare.

An harba tauraron mai suna Gaofen-13 ne bisa amfani da rokar Long March-3B.

Tauraron zai taimakawa aikin raya tattalin arziki ne ta hanyar samar da bayanai. Muhimman ayyukansa sun hada da safayon kasa da kiyasin amfanin gona da kare muhalli da hasashen yanayi da kuma bada gargadin wuri tare da kare aukuwar annoba.

Wannan shi ne karo na 349 da aka yi amfani da samfurin rokar Long March wajen harba tauraron dan Adam. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China