Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Falasdinu ta shiryawa gudanar da zabuka nan bada dadewa ba
2020-10-12 14:15:02        cri
Firaministan Falasdinu, Mohammed Ishtaye, ya bayyana a jiya cewa, Falasdinu ta shiryawa gudanar da sahihin zabe bisa tsarin demokradiyya nan bada dadewa ba.

Mohammed Ishtaye ya bayyana yayin bikin lokacin girbi a Ramallah cewa, za a yi bikin murna a kasar, bayan an gudanar da zabuka da nufin dawo da gwamnatin kasar.

Ya ce dukkan Falasdinawa za su hadu karkashin majalisar dokokin kasar cikin hadin kai, kamar yadda yake a baya, karkashin kungiyar 'yantar da Falasdinawa ta PLO, domin tsayar da kasar da kafarta.

Ana sa ran babban zaben kasar zai gudana tsakanin watan Fabreru zuwa Maris na 2021. A baya, an shirya gudanarwa ne a shekarar 2014 kamar yadda yarjejeniyar kungiyoyin Fatah da Hamaz ta Gaza, ta tanada a wancan lokacin.

Sai dai, an dage zabukan har sai baba-ta-gani. A watan Oktoban 2017 kuma, Hamaz da Fatah suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a Gaza, inda Hamas ta amince a rushe gwamnatin hadin kan kasa tare da gudanar da zabuka a karshen shekarar 2018, sai dai kuma har ila yau, ba a gudanar da zabukan ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China