Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Falasdinu ta yi barazanar dakatar da amincewa da halaccin Isra'ila idan ta ci gaba da aiwatar da shirinta na mamaya
2020-06-09 09:46:16        cri
Firaministan Falasdinu, Mohammed Ishtaye, ya yi gargadin cewa, gwamnatin Falasdinu za ta dakatar da amincewa da halaccin Isra'ila muddin ta ci gaba da shirinta na mamaye yankunan Falasdinu.

Mohammed Ishtaye ya bayyana yayin wata hira a gidan talabijin na kasar cewa, batun dakatar da amincewa da halaccin Isara'ila, zai ci gaba da kasancewa, muddun Isra'ila ta ci gaba da kudurinta na mamaya.

Ya kara da cewa, mamaye wasu sassan yankin kogin Jordan da Isra'ila ta yi, na da nufin kawo tsaiko ga yuwuwar kafa 'yantacciyar kasar Falasdinu.

Firaministan ya kara da cewa, kasashen duniya sun fahimci matakin Falasdinu na kauracewa yarjeniyoyi da fahimtar da aka cimma tsakaninta da Isra'ila, saboda sun san cewa Isra'ila ta yi gaban kanta wajen daukar matakin mamaye yankunan Falasdinu.

Ya kuma tabbatar da cewa, bangaren Falasdinu ya dakatar da dukkan wata hadin gwiwa da Isra'ila a fannonin da suka shafi tattalin arziki da kiwon lafiya da tsaro. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China