Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Ba wanda zai lahanta dangantakar Afrika da Sin
2020-10-10 15:29:39        cri

A kwanakin baya, farfesa Sheriff Ghali Ibrahim ya wallafa wani sharhi a jaridar Leadership mai taken "Dudduba dangantakar Afrika da Sin", inda ya yi Allah wadai da ra'ayoyin dake batanci ga kasar Sin da ma dangantakar dake tsakaninta da Afrika. A ganinsa, kasar Sin abokiyar nahiyar Afrika ce, kuma Afrika za ta ci gajiyar hadin kan bangarorin biyu, nuna kiyayya ga kasar Sin zai lahanta hadin kan bangarorin biyu.

Bayanin ya nuna cewa, sharhin da mai nazarin manufofin Afrika da gabas ta tsakiya na asusun ba da lamuni na Amurka ya bayar mai taken "Mai yiwuwa kasar Sin na leken asiri kan gine-ginen gwamnatin Afrika" ba shi da wani shaida ko kadan.

Bayanin ya ce, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taba bayyana cewa, ba wata kasa da take taimakawa Najeriya tun bayan da ta samu 'yancin kai kamar Sin. Shi ma a nasa bangare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, ba wanda zai lahanta hadin kan jama'ar bangarorin biyu.

Bayanin ya kara cewa, Sin tana baiwa nahiyar tallafin jin kai ba tare da wani sharadi ba, kuma tana iyakacin kokarin taimakawa nahiyar wajen yaki da cutar Ebola da COVID-19. Ya ce kasashen Afrika na zaba hanyar da za su bi, wato hada hannu da kasar Sin, da ma ci gaba da raya dangantakar bangarorin biyu duk da ganin sauyawar halayen kasa da kasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China