Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'ar kula da harkokin mata ta MDD ta yabawa nasarorin da Sin ta cimma wajen kare hakkin mata
2020-09-27 16:56:08        cri

Mataimakiyar babban sakataren MDD, kana babbar daraktar kula da al'amurran mata ta MDD, Phumzile Mlambo-Ngcuka, ta yabawa nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen kare hakkin mata, kana ta karfafawa kasar gwiwa inda ta bukaci Sin ta kara himma.

Kasar Sin ta samar da muhimman damammakin ga mata da yara 'yan mata ta fuskar samar da guraben ayyukan yi da fannin ilmi, Mlambo-Ngcuka ta bayyana hakan ne a wata muhimmiyar tattaunawa gabanin babban taron MDD game da cika shekaru 25 da gudanar da taron matan duniya a karo na hudu a birnin Beijing.

Tace tun a shekarar 2012, kasar Sin tayi nasarar tsame mata kusan miliyan 41 daga kangin talauci ta hanyar kirkiro damammakin guraben aiki yi domin samar musu kudaden shiga da ayyukan dogaro da kai.

A cewar jami'ar, an samu gagarumin cigaba wajen ilmantar da yara mata da kuma matasa mata, da kashi 99.9 bisa 100 na matan da aka shigar da su makarantun firamare, da kuma mata matasa wanda ya kai sama da kashi 50 na yawan daliban da aka baiwa ilmi na manyan makarantun kasar, yayin da aka samu kashi 52.5 bisa 100 na matan dake karatun digirin farko.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China