Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gidan talabijin na PBS SoCal dake Amurka ya watsa wani shirin da gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ya tsara game da kawar da talauci
2019-08-02 19:52:12        cri

 

An watsa wani shirin musamman dangane da yadda kasar Sin ke nuna himma da kwazo wajen yaki da talauci, a gidan talabijin na PBS SoCal dake kasar Amurka a ranar 31 ga watan Yuli, wanda ya kasance karon farko da wani muhimmin gidan talabijin na Amurka ya watsa irin wannan shiri na musamman, a game da yadda gwamnatin kasar Sin ke tallafawa matalauta a idon wani dan kasar Amurka.

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya yi shekaru biyu yana tsara wannan shirin TV mai suna "Ziyarar gani da ido: Yadda kasar Sin ke yaki da talauci" ko kuma "Voices from the Frontline: China's War on Poverty" a turance, inda masu daukar hoton bidiyo suka ziyarci wasu magidantan dake fama da talauci, a lardunan Guizhou, da Gansu, da Shanxi, da Sichuan, da Hainan, gami da jihar Xinjiang ta kasar Sin, da nunawa masu kallo dimbin nasarorin da kasar ta samu wajen yaki da talauci, gami da wasu matsalolin da har yanzu ake fuskanta a wannan fanni.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China