Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin yaki da ta'addanci na MDD zai bude cibiya a Morocco
2020-10-07 16:24:35        cri
Ofishin yaki da ayyukan ta'addanci na MDD ko UNOCT a takaice, ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da gwamnatin kasar Morocco, wadda ta shafi kafa wata cibiya da za ta aiwatar da shirin samar da dabarun yaki da ta'addanci, da hadin gwiwa tsakanin ofishin da masu ruwa da tsaki na nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labarai na Morocco MAP, ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne, yayin taro ta kafar bidiyo, tsakanin sakataren ofishin na UNOCT Vladimir Voronkov, da kuma ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita.

Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, Mr. Voronkov ya ce, ofishin UNOCT zai samar da horo ga jami'ai a fannin yaki da ta'addanci, da kare doka, da tsaron kan iyakoki, da kandagarkin yaduwar masu tsattsauran ra'ayi, da alakar kare hakkin bil Adama da yaki da ta'addanci.

Jami'in ya ce, cibiyar da za ta gudanar da wannan aiki na da kwarewa, daidai da bukatar nahiyar Afirka, wadda za ta baiwa kasashen nahiyar damar daga matsayin ayyukan su na yaki da ta'addanci, ta yadda za su ci gaba da aiki bisa kwarewa.

A nasa bangare kuwa, Mr. Bourita ya ce cibiyar, za ta tunkari kalubalolin dake addabar nahiyar Afirka a fannin karuwar barazanar ta'addanci, tare da fatan za ta karfafa kwarewar kasashen da za su shiga wannan aiki, ta yadda za su amfana daga horon gina sanin makamar aiki a fannin na yaki da ta'addanci yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China