Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Morocco ita ce kasa mafi zuba jari a yankin yammacin nahiyar Afrika
2019-11-21 10:17:47        cri
Ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita, ya bayyana cewa, tsakanin kasashen dake nahiyar Afirka, Morocco ita ce kasa mafi zuba jari a yankin yammacin Afrika, Kuma kasa ta biyu mafi zuba jari a daukacin nahiyar.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Morocco ta fitar a jiya, ta ruwaito Nasser Bourita ya bayyana yayin taro karo na 3 na shirin hadin gwiwar kungiyar G20 da kasashen Afrika wato (CwA), wanda ya gudana a birnin Berlin cewa, kusan 2 bisa 3n jarin Morroco na kai tsaye na tafiya ne ga kasashen nahiyar.

Ya ce nahiyar Afrika da ci gabanta, muhimman abubuwa ne dake kan gaba cikin manufofin Morocco na ketare.

Nasser Bourita ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci a kara fadada taron na CwA ta hanyar kara bude kofa ga kasashen Afrika da kawar da wariyar da ake nuna bisa tunanin cewa kasuwanninsu sun fi hadari, tare kuma da karfafa dagantaka tsakanin kasashen nahiya guda da kuma na nahiyoyi daban daban.

Taron CwA ya samo asali ne a shekarar 2017 a lokacin da Jamus ke shugabantar kungiyar G20, da nufin inganta zuba jari a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China