Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin Amurka na matsa lamba ga kamfanonin wasu kasashe danniya ne
2020-10-01 20:47:59        cri

 

A ranar 27 ga watan Satumba, wata kotun tarayyar Amurka dake gundumar Columbia, ta yanke hukuncin yin watsi da umurnin gwamnatin Amurka na neman daina amfani da manhajar Tik Tok a wayoyin hannu a Amurka. Kwararru a fannin suna ganin cewa, batun Tik Tok magana ce kawai, Amurka ba ta taba gabatar da wata hujja ba game da matsin lamba da take nuna wa kamfanonin wasu kasashen. Nan gaba kuma, Amurka na iya shakkar kamfanonin sauran kasashe bisa wannan dalili.

 

 

Mataimakin shugaban kwalejin nazarin tsaron harkokin sadarwa na kasar Sin Zuo Xiaodong ya ce, "matakin Amurka na matsawa kamfanonin wasu kasashe rashin kan gado ne, kuma ya keta ci gaban wayewar kan al'ummar dan Adam." A ganinsa, gwamnatin Amurka ba za ta daina irin wannan mataki ba idan ba ta cimma burinta ba, wato ba za ta canja shirinta ba sakamakon hukunci da wata kotu ta yanke. Kasar Amurka ba ta taba ba da shaidu ba a yayin da take shakkar wai kayayyakin wasu kasashe suna kawo barazana ga tsaron ta, kuma ba ta girmama sauran kasashe, tana abin da take so, wannan ra'ayin danniya ne. Amma, matakin matsawa kamfanonin wasu kasashe lamba, a hakika mataki ne na kokarin kawar da sabbin fasahohi.

Mujallar Harvard Business Review ta rubuta cewa, umurnin haramta Tik Tok ya kara bayyana cewa, kasar Amurka ba za ta martaba tsarin cinikayyar duniya ba, kuma wannan boyayyen kalubale ne, irin wannan ra'ayi na canja tsarin tattalin arzikin duniya da ma yin tasiri ga kamfanonin kasar ta Amurka."(Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China