Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manakisar wasu Amurkawa na yi wa TikTok fashi ba zai yi nasara ba
2020-09-26 21:54:50        cri

A cewar wasu rahotanni na baya-bayan nan, Uwar kamfanin Tik Tok, wato ByteDance na kasar Sin da kamfanonin Oracle da Wal-Mart na Amurka, sun cimma yarjejeniya. Sai dai, a cewar Amurka, akwai rashin daidato a cikin yarjejeniyar.

A cewar yarjejeniyar da Amurka ta gabatar, sabon kwamitin gudanarwar Tik Tok za ta kunshi mutane 5, 4 daga cikinsu Amurkawa, mutum daya ne kadai zai kasance Basine. Sannan kwamitin zai kunshi wani daraktan hukumar tsaro, wanda nadinsa zai dogara da amincewar gwamantin Amurkar. A hannu guda kuma, kamfanin Oracle na da damar sake nazarin kamfanin Tik Tok da sauran karin wasu abubuwa.

Ana iya ganin cewa, yadda 'yan siyasar Amurka ke farwa wasu harkokin kasuwanci kamar Tik Tok, abu ne da aka tsara domin cin zalin kamfanonin da ba na kasar ba, wadanda ke gaba-gaba a wasu fannoni. Kuma wannan na nufin 'yan siyasar Amurka sun matsawa Tik Tok a yau, a gobe kuma, za su mayar da hankali kan sauran kamfanoni baki dake gogayya da Amurka.

A zamanin da ake ciki yanzu, babu wata kasa da ke da karfin amfana ita kadai daga ci gaban duniya, bare kuma ta yi gaban kanta wajen yin babakere da cin zali da mulkin mallaka. Kasar Sin ba za ta amince da duk wata yarjejeniya dake katsalandan cikin harkokin tsaronta, da mutunci da kuma daddaden ci gaban kamfanoninta ba. Wannan ba ya nufin kare muradunta, sai dai, kare hakkokin kasashe da kamfanonin da Amurka ke cin zali. Shirin yi wa TikTok fashi ba zai taba nasara ba! (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China