Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan wajen Gambia ya ba da tabbacin ci gaba da hadin gwiwa da Sin
2020-09-30 11:50:32        cri

Ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Gambiya Mamadou Tangara, ya bayar da tabbacin ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasarsa da kasar Sin a yayin da ofishin jakadancin kasar Sin dake Banjul ya shirya bikin murnar cika shekaru 71 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Ya ce gwamnatin kasar Gambiya a ko da yaushe tana goyon bayan karfafa tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban, da hadin gwiwar moriyar juna, da shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma tattabar da ci gaban ajandar hadin gwiwar dandalin Sin da Afrika wato FOCAC.

Haka zalika, Tangara ya ce, za su ci gaba da goyon bayan al'ummar Sinawa, wajen martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, ya bayyana hakan ne a lokacin gabatar da jawabi a taron ta kafar intanet.

Ministan na Gambiya ya ce, a yayin da ake ci gaba da kokarin tsara manufofin raya ci gaban kasa, tilas ne a amince da yin hadin gwiwa da kasar Sin a ko wane lokaci, ya kara da cewa, ta hadin gwiwa tare da juna ne za a samu karfi, kuma ta hanyar hadin gwiwa ne za a samar da muhallin ci gaban duniya mafi dacewa.

Kasashen Gambia da Sin sun maido da huldar diflomasiyya a tsakaninsu a shekarar 2016. Tun daga wancan lokacin, Gambia da Sin sun kaddamar da muhimman ayyukan raya ci gaba domin taimakawa karamar kasar ta yammacin Afrika.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China