Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu bore a Gambiya na neman shugaban kasar ya yi murabus
2019-12-17 15:17:00        cri

Dubban mutane ne suka shirya wata zanga-zanga a Banjul, babban birnin kasar Gambiya a jiya Litinin, inda suke neman shugaban kasar Adama Barrow da ya yi murabus, bayan cika wa'adin mulkinsa na shekaru uku, kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zaben shekarar 2016.

Kundin tsarin mulkin kasar dai, ya kayyade wa'adin shekaru biyar ne, Ko da yake, a lokacin yakin neman zaben shugaban kasar na shkekarar 2016, Barrow ya yi alkawarin cewa, idan har aka zabe shi, shekaru uku kacal zai yi a kan mulki. Ya kuma cimma yarjejeniya kan wannan alkawari da abokan kawancensa na gamayyar jam'iyyun dake mulkin, abin da ke zama na wucin gadi kafin a kira zabuka.

A watan Maris, Barrow ya shirya gudanar da zabe a shekarar 2021, bayan ya kammala wa'adin mulkinsa, sai dai jam'iyyun hadaka sun yi watsi da shirin shugaban.

Masu zanga-zangar na kira ga shugaba Barrow da ya cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe ya yi murabus.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China