Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
" Raba gari ta fannin kimiyya da fasaha" da kasar ta Sin? Lallai wasa ne irin na wauta
2020-09-29 21:17:19        cri
"Mai yiwuwa ne Amurka ba za ta yi nasara ba a 'yaki da kasar Sin a fannin kimiyya da fasaha'." James Kynge, kwararren 'dan jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ya bayyana haka ne a cikin sharhin da ya rubuta kwanan baya, inda ya ce, matsalar da Washington ke fuskanta ita ce, yadda take matsawa kamfanonin kasar Sin lamba a fannonin kimiyya da fasaha, zai lahanta kasar Amurka.

A 'yan kwanakin da suka wuce, 'yan siyasar kasar Amurka suna ta furta kalaman " Raba gari a fannin kimiyya da fasaha" da kasar ta Sin, da kuma kara cin zarafin kamfanonin kasar. Amma, kamar yadda manazarta suka nuna, cewa Amurka ba za ta amfana ba da wannan mataki.

Da farko, tsorata da matsa lamba kan kamfanonin kasashen waje da gwamnatin kasar Amurka ta yi, a hakika ya nuna cewa, ana kara mayar da kasuwar kasar a matsayin wani batun siyasa, hakan bai dace ba a zuba jari a kasar.

Na biyu, a bisa matakan da gwamnatin kasar ta dauka, akwai alamar "mayar da batun siyasa" kan kayayyakin cinikayyar kasar Amurka, ko shakka babu, hakan zai rage karfin takara na kayayyakin kasar.

Ban da wannan kuma, cikin makonni 2 da suka wuce, kamfanonin kasar Amurka kimanin 3500 sun shigar da kara a kotu, bisa zargin matakin da gwamnatin shugaba Trump ta dauka, na kara sa haraji kan kayayyaki kirar kasar Sin, wadanda darajarsu ta zarce dalar Amurka biliyan 300, da cewa ya saba doka.

 

 

Matakin da kasar Amurka ta dauka ba zai hana ci gaban kasar Sin a fannonin kimiyya da fasaha ba, a maimakon haka ma, zai zaburar da kasar wajen kara saurin yin kirkire-kirkire a wadannan fannoni.

Yanzu dai kasar Sin na gaggauta nazari kan wasu fannonin da suka shafi muhimman fasahohi. Kamar yadda wani sharhi kan harkokin kasashen waje, cewa kasar Sin ta shirya na dogon lokaci don tinkarar matsin lamba daga Amurka a fannonin kimiyya da fasaha. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China