2020-09-24 20:51:10 cri |
Wasu rahotannin baya bayan nan sun hakaito sakataren wajen Amurka Pompeo, yana zargin kasashen Sin, da Iran, da Venezuela da wasu karin kasashen, da laifin keta hakkokin bil Adama. Game da hakan ne kuma Mr. Wang Wenbin ya amsa tambayar da aka yi masa, inda ya ce Amurka ta sha nada kanta malamar kare hakkin bil Adama, tare da zargin sauran kasashe da keta hakkin bil Adama. Duk kuwa da cewa Amurkan na cikin mummunan yanayi na kare hakkin bil Adama.
Bugu da kari, a cewar rahoton, Mr. Pompeo ya bukaci Amurka da jami'an ta, da su yi taka tsantsan da jami'an diflomasiyyar kasar Sin, don kaucewa amfani da su wajen yada farfagandar Sin da ma leken asiri. Da yake maida martani game da hakan, Wang Wenbin ya ce 'yan siyasar Amurka na fama ne da dimuwa sakamakon kin jinin Sin, kuma kasar Sin ba ta taba damuwa da harkokin cikin gidan Amurka ba. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China