Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Filin jiragen saman babban birnin Najeriya ya dawo da jigilar kasa da kasa bayan rufe shi na tsawon watanni 6
2020-09-08 14:21:59        cri
A ranar Litinin an bude sashen sufurin jiragen sama na kasa da kasa a filin jirgin saman babban birnin Najeriya, an fara aikin sufurin jiragen saman karo na farko bayan shafe watanni shida da dakatarwa sakamakon bullar annobar COVID-19.

Jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines, mai dauke da fasinjoji 120 da ma'aikatan jirgin 13, ya sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe dake Abuja, da misalin karfe 1:32 na rana agogon kasar, daidai da karfe 12:32 agogon GMT, kamar yadda jami'an kasar suka bayyana.

Wannan ne karo na farko da aka samu saukar jirgi a filin jirgin saman kasar tun daga ranar 23 ga watan Maris bayan da aka rufe dukkan filayen jiragen saman kasar a matsayin matakan dakile yaduwar annobar COVID.

Kwararrun masana harkokin sufurin jiragen saman Najeriya, da jami'an kasar, sun bayyana dawo da harkokin sufurin jiragen saman kasa da kasa a matsayin wani babban ci gaba ga bangaren kamfanonin sufurin jiragen sama a kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China