Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu tsoffin shugabannin kasashen duniya sun yi kira da a karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin yaki da cutar COVID-19
2020-09-03 14:55:20        cri
A ranar 31 ga watan Agusta, kungiyar hadin gwiwar kwararru kan shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shirya wani taron karawa juna sani na kwararrun kasa da kasa ta kafar bidiyo. Babban taken taron shi ne "Daidaita bambancin ra'ayoyi, domin gina makomar bil Adama ta bai daya". A yayin taron, wasu tsoffin shugabannni da kwararru na kasashen duniya sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu, inda suka yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya.

Tsohon shugaban kasar Slovenia Danilo Turk ya bayyana cewa, akwai bukatar kasashen duniya su daidaita bambancin ra'ayin dake tsakaninsu. Yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 matsala ce dake gaban duniya baki daya, kuma hanyar yin hadin gwiwa ita ce hanya kadai da za a warware wannan matsala kamar yadda ake fata. Kuma, yin hadin gwiwa ita ce muhimmiyar dabarar daidaita bambancin ra'ayoyi a tsakanin kasa da kasa, amma, ra'ayin kishin kasa da wasu kasashen suke nunawa ya kawo matsala ga hadin gwiwar kasa da kasa.

A nasa bangare, tsohon firaministan kasar Masar Essam Sharaf ya ce, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta samar da dandalin habaka hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, ta yadda kasashen duniya za su hada kai wajen raya tattalin arziki da fuskantar kalubaloli. Ya ce, a halin yanzu, wannan shawarar da kasar Sin ta gabatar, ta kasance shawarar kasa da kasa.

Haka kuma a yayin taron, an gabatar da shawarar "karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kara gina makomar bil-Adam ta bai daya" da kwararrun kasa da kasa da Sin kimanin 200 suka tsara cikin hadin gwiwa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China