Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Afirka da Sin sun hada kai wajen yaki da cutar COVID-19 da kara sada zumunta
2020-09-01 10:21:45        cri

A jiya ne farfesa Agaba Halidu, shaihun malamin siyasa da dangantakar kasa da kasa na Jami'ar Abuja dake tarayyar Najeriya, ya gabatar da wani sharhi a jaridar Peoples Daily, mai taken "Hada kai don yaki da cutar COVID-19 tsakanin Sin da Afirka", inda ya ce kasashen Afirka da Sin, sun nunawa juna goyon baya cikin dogon lokaci.

Malamin ya ce bayan abkuwar cutar COVID-19 a nahiyar Afirka, Sin ta tura tawagogi don taimakawa kasashen nahiyar, kana kasashen Afirka da Sin, sun kara sada zumunta da juna a sakamakon hada kai wajen yaki da wannan cuta.

Sharhin ya bayyana cewa, Sin ta dora muhimmanci ga nahiyar Afirka, kuma mu'amala da hadin gwiwa dake tsakanin bangarorin biyu na da dadadden tarihi. Ya ce bayan barkewar cutar COVID-19, Sin ta yi kokari matuka wajen daukar matakan magance yaduwar cutar a dukkan fannoni, inda ta kai ga dakile yaduwar cutar cikin nasara. A lokacin kuma, kasashen Afirka da dama sun nuna goyon baya gare ta, wanda hakan ya shaida zumunta mai zurfi dake tsakanin sassa biyu.

Bisa yanayi mai tsanani na tinkarar cutar a nahiyar Afirka, Sin ta zama ta farko wajen tura tawagar likitoci zuwa Afirka don taimakawa yaki da cutar, da more fasahohin yaki da cutar, ta kuma tura kayayyakin yaki da cutar da dama zuwa kasashen Afirka a karo daban daban. Kana Sin ta yi alkawarin cewa, bayan cimma nasarar nazari kan allurar rigakafin cutar COVID-19, da samar da ita, kasashen Afirka za su zama kan gaba wajen cin gajiyar rigakafin.

Bugu da kari, sharhin ya ce, Sin ta fara taimakawa kasashen Afirka a fannin likitanci a shekarar 1963, ya zuwa yanzu dai ma, yawan ma'aikatan jiyya da Sin ta tura zuwa Afirka ya kai dubu 243, wadanda suka bada jinya ga marasa lafiya miliyan 220 a kasashen nahiyar. Sakamakon wannan annobar da ke fama da ita, an kara zurfafa zumunci a tsakanin Afirka da Sin, da kuma hadin gwiwar dake tsakaninsu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China