Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe na daukar matakan farfado da fannin hakar ma'adanai
2020-08-09 15:29:17        cri
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya ce ana sa ran kamfanonin hakar ma'adanan kasar za su bada gudunmawa na kusan dala biliyan 12 ga tattalin arzikin kasar nan da shekarar 2023 yayin da gwamnatinsa ke kokarin daukar matakan farfado da fannin.

Mnangagwa ya yi wannan tsokaci ne a lokacin sake kaddamar da zuba jarin kamfanin Anjin, wani kamfanin aikin hakar ma'adanai ne na hadin gwiwar Sin da Zimbabwe, dake yankin Chiadzwa mai arzikin lu'u-lu'u dake lardin Manicaland.

Shugaba Mnangagwa ya ce yana da tabbatacin cewa kamfanin Anjin zai bayar da gudunmawa wajen farfado da aikin hakar ma'adanin lu'u-lu'u a kasar Zimbabwe saboda irin kwarewar da kamfanin ke da shi.

Ya ce suna kuma kokarin lalibo hanyoyin da za'a samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba, da kuma wasu damammakin samar da hanyoyin dogaro da kai ga jama'a karkashin wannan fanni na aikin hakar ma'adanai.

Zimbabwe tana fadi tashin amfani da fannin hakar ma'anai a matsayin muhimmin bangaren da zai taimaka mata wajen farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya durkushe sakamakon tashin farashin kayayyaki da karancin kudaden musaya da kasar ke fuskanta. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China