2020-09-04 20:05:14 cri |
Mai magana da yawun harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, ita ce ta bayyana haka Jumma'ar nan, yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Rahotanni na cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta fitar da wani sabon bayani game da Xinjiang, inda ta soki manufar kasar Sin game da kare hakkin bil-Adam, da batun addini, da sauran batutuwa a Xinjiang, gami da sanya aikin dole da tilasta takaita iyali.
Yayin da take amsa tambayoyi game da wadannan batutuwa, Hua Chunying ta jadadda cewa, batutuwan da suka shafi Xinjiang, ba su da nasaba da kungiyoyin kabilu, ko addini, ko 'yancin bil-Adama, amma batu ne da ya shafi yaki da ta'addanci da 'yan aware. Yankin ya bulla da matakan kawar da matsalar ta'addanci da sauya tunanin masu tsattsauran ra'ayi, ta hanyar bullo da shirin samar da ilimi da koyar da sana'o'i da sauran hanyoyi, matakan da suka kai ga nasarar magance yawaitar aukuwar ayyukan ta'addanci a yankin, da tabbatar da 'yancin yin rayuwa, da samun kiwon lafiya da ci gaban dukkan kungiyoyin kabilu.
Rabon a kai wani harin ta'addanci a yankin, tun kusan shekaru hudu da suka gabata. (Ibrahim Yaya)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China