Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bai dace masu adawa da kasar Sin su rika yada jita-jita game da Xinjiang ba
2020-09-02 21:06:02        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta yi watsi da ikirarin da masu adawa da kasar Sin ke yi cewa, wai gwamnatin kasar Sin tana musgunawa 'yan kabilar Uygur da ma neman rage yawan kabilar ta Uygur. Madam Hua ta yi nuni da cewa, a shekarar 2018, yawan 'yan kabilar ta Uygur a yankin Xinjiang, ya kai miliyan 12.71, adadin da ya ninka fiye da na shekaru 40 da suka gabata, a don haka ta yaya aka samu karuwar wannan adadi idan har ana kisan kare dangi?

Hua Chunying ta bayyana cewa, bayanan da masu adawa da kasar Sin suke amfani da su wajen bata manufofin kasar Sin game da Xinjiang, galibi sun fito daga wajen Zheng Guoen, wani masani makiyin kasar Sin, wanda yake rayuwa ta hanyar yada jita-jita game da Xinjiang da neman bata sunan kasar Sin.

Kasar Sin tana adawa da yada jita-jita marasa tushe, da yada jita-jita bisa son rai da kuma zato ba tare da kwararan shaidu ba. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China