Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafafen Watsa Labaran Kasa Da Kasa Sun Yi Ta Yada Rahotannin Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin
2020-09-03 15:17:51        cri

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya kuma take da ingantaccen tsarin kandagarki da shawo kan annobar COVID-19, kana kasa ta farko a duniya da ta maido da ayyukan masana'antunta, matakan da kasar Sin take cigaba da dauka domin raya tattalin arzikinta ya ba ta damar zama a sahun gaba wajen zama jagorar karfin tattalin arziki a duniya. Kwanaki kadan da suka gabata, kafafen yada labarai daban daban na duniya sun yi ta yabawa irin nasarorin da Sin ta samu game da farfadowar tattalin arzikin kasar, suna masu bayyana cewa, kasar Sin za ta iya zama a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya bisa nasarorin da ta samu na bunkasuwa a shekarar 2020.

Jaridar The New York Times ta Amurka ta wallafa wani sharhin dake cewa, "babbar bunkasuwar" fitar da kayayyaki zuwa ketare tun bayan farfadowa mafi girma na masana'antun sarrafa hajoji na kasar Sin a karshen watan Fabrairu kuma har yanzu karfin tattalin arzikin karuwa yake.

Adadin fitar da kayayyakin Sin zuwa ketare ya karu da kashi 10.4% idan an kwatanta da watan Yulin bara, kuma shi ne farfadowa mafi girma a duniya tun bayan barkewar annobar, kamar yadda alkaluman da babbar hukumar aikin kwastam ta kasar Sin ta fitar.

Sin, kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, ta yi matukar farfadowa daga tasirin annobar COVID-19, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters. Idan an kwatanta da fannin masana'antu, kamfanonin ayyukan hidima na kasar Sin sun yi matukar fadada sannu a hankali, kuma karfin da suka samu ya kara bunkasa tattalin arzikin kasar.

A bisa alkaluman wani binicke da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a ranar 31 ga watan Ogasta ya nuna cewa, ma'aunin tattalin arzikin PMI na ayyukan hidima a watan Ogasta a kasar ya kai kashi 54.3 bisa 100, inda ya karu da kashi 1.2 bisa 100 idan an kwatanta da na watan Yuli.

A baya-bayan nan, mujallar The Wall Street Journal ta fitar da wasu jerin yabo na irin nasarorin da tattalin arzikin kasar Sin ya cimma, inda sharhin ya kara da cewa, ana tsammanin tattalin arzikin kasar Sin ne kadai ya samu nasarar bunkasa a cikin wannan shekara.

Tattalin arzikin kasar Sin ya karu cikin sauri a rubu'i na biyu na wannna shekara, tilas ne a yabawa tsare-tsare da manufofin tallafawa tattalin arzikin kasar, in ji mujallar ta The Wall Street Journal. Muhimman matakai da manufofin gudanar da al'amurran kudi da kasar Sin ta bullo da su za su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa tattalin arzikin kasar Sin don samun farfadowa, kuma za su ci gaba da taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin kasar nan da wasu shekaru biyu masu zuwa.

Bisa samun farfadowar tattalin arzikin masu saye da sayarwa na kasar Sin, mafi yawan cinikin da kamfanoni mallakin 'yan kasashen waje suka yi a kasar Sin ya yi matukar karuwa sabanin yadda aka yi hasashe, ba ma kawai hasashen samun hasara sakamakon raguwar cinikinsu ba, har ma kayayyaki kirar kasar Sin sun samu matukar karbuwa a wajen kamfanoni na duniya masu yawan gaske kamar kamfanonin Nike da Tesla. (Mai Fassarawa: Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China