Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi Jinping ya ajiye fure don martaba wadanda suka sadaukar da rayukan su yayin yakin kin jinin harin Japanawa
2020-09-03 11:35:43        cri
A yau Alhamis ne ake cika shekaru 75, tun bayan da al'ummun Sinawa suka yi nasarar yakin kin jinin harin Japanawa, kuma ita ce ranar cika shekaru 75, da al'ummun kasa da kasa suka yi nasarar yakin kin tafarkin murdiya.

Albarkacin wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran manyan jami'an JKS, da jagororin gwamnati, sun taru a babban dakin taruwar jama'a na tunawa da yakin kin jinin harin Japanawa.

Shugabannin na Sin, da sauran al'ummu daga sassan rayuwa daban daban na kasar, sun jigine furanni, a matsayin alamar jinjinawa wadanda suka sadaukar da rayukan su, domin kare kasar Sin daga maharan Japan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China