Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi Jinping ya taya Sarkin kasar Malaysia murnar cika shekaru 63 da samun 'yancin kan kasar sa
2020-08-31 14:18:00        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Sultan Abdallah na kasar Malaysia, murnar cika shekaru 63 da samun 'yancin kan kasar sa. Shugaba Xi wanda ya zanta da Sultan Abdallah ta wayar tarho a yau Litinin, ya jaddada muhimmancin shawarar nan ta "ziri daya da hanya daya", yana mai cewa, da hadin gwiwar Sarki Abdallah, sassan biyu za su iya zurfafa cikakkiyar hadin gwiwa daga dukkanin fannoni tsakanin Sin da Malaysia.

Kaza lika za su samu zarafin gina hadin gwiwa mai inganci, wadda dukkanin sassan biyu za su ci gajiyar ta, tare da ba da gudummawa ga ci gaba, da kyautatuwar zamantakewar al'ummunsu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China