Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka zata sanya takunkumi kan manyan jami'an kotun ICC
2020-09-03 11:26:36        cri
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya sanar cewa gwamnatin Amurka zata sanya takunkumi kan babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, Fatou Bensouda, da shugaban sashen gudanar da mulki da hadin gwiwa, Phakiso Mochochoko.

Pompeo ya fada a taron manema labarai a wannan rana cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya shinge na bayar da takardun biza ga daidaikun mutanen dake da hannu wajen binciken wasu jami'an Amurka, kuma mutane da hukumomin dake cigaba da samar da tallafi ga mutanen da ake sanya musu takunkumin ma zasu iya fuskantar takunkumin.

A watan Maris, kotun ICC ta kaddamar da bincike kan zargin aikata laifukan yaki, da cin zarafin dan adam a kasar Afghanistan, wanda ya shafi kungiyar Taliban, da jami'an tsaron Afghanistan, da sojojin Amurka, da jami'an tattara bayanan sirri da ake tuhuma. Bensouda ya ce, akwai isassun hujjoji dake nuna cewa jami'an Amurka dake Afghanistan tsakanin shekarun 2003 zuwa 2004 sun gallazawa mutanen da aka tsare, da keta musu haddi, da sauran laifuka.

A watan Yuni, shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya gabatar da takardar umarni daga fadar shugaban kasa inda ya bayyana cewa, Amurka ta tsame hannunta daga duk wasu harkokin da suka shafi kotun ICC, inda ya nuna cewa, duk wani batu dake shafar binciken da kotun ke yiwa sojojin Amurka da jami'an leken asirinta dake Afghanistan tamkar yin barazana ce ga ikon mulkin Amurka da tsaron kasar da kuma harkokin diflomasiyyarta, har ma gwamnatin Amurkar ta yi ikirarin sanya takunkumi kan duk wasu jami'an dake da hannu kan wannan batu.

A baya, kafar yada labaran Amurka ta bada rahoton cewa, kasar Afghanistan tana da hulda da kotun ta ICC, hakan ya tabbatar da cewa kotun ICC ke da hurumin hukunta laifukan da ake batu a kan su a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China