Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Ya kamata Sin da Jamus su yi hadin gwiwar yaki da annoba tare da taimakawa farfadowar tattalin arziki
2020-09-02 10:53:54        cri
Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce a halin da ake ciki, duniya na fuskantar muhimman zabi uku, yayin da a na su bangare, kasashen Sin da Jamus, dake matsayin kasashe masu fada a ji, ya dace su yi hadin gwiwa wajen aiwatar da wasu ayyuka uku.

Wang ya bayyana hakan ne jiya Talata, cikin wata sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa da takwaransa na kasar Jamus Heiko Maas, a wani bangare na ziyarar aiki da yake yi a Jamus. Wang ya ce sun gudanar da tattaunawa mai zurfi, mai ma'ana ta kawance, wadda ta habaka amincewa da juna, tare da haifar da sakamako mai armashi.

A cewar ministan, aiki na farko dake gaban kasashen biyu, shi ne bunkasa matakan hada kai don yakar cutar COVID-19, da kuma bunkasa farfadowar tattalin arzikin duniya.

Abu na biyu kuma, shi ne kara daidaita yanayin alakar kasashen, da daga matsayin dangantakar su zuwa mataki na gaba. Sai kuma bukatar yin aiki tare, don goyon bayan cudanyar sassa daban daban, da watsi da manufar yakin cacar baka. Wang ya ce kasashen biyu ba sa goyon bayan ruwa wutar gaba, da yin fito na fito, za su kuma mara baya ga karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin kasa da kasa, kana za su taimakawa MDD da WHO da ma manufar cudanyar kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China