Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kalaman Xi Jinping dangane da Yakin Kin Harin Sojojin Japan
2020-09-01 19:25:28        cri

A wannan shekara, ake cika shekaru 75 da jama'ar kasar Sin suka samu nasarar Yakin Kin Harin Sojojin Kasar Japan. A don haka, ya dace a waiwayi kalaman da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada dangane da wannan shahararren yaki.

Shugaba Xi Jinping ya fada a baya cewa: "Nasarar da jama'ar kasar Sin suka samu a yakin da suka gabza da maharan kasar Japan, ita ce irinta na farko da Sinawa suka samu kan sojojin kasashen waje da suka kawo hari ga kasar Sin. Wannan nasara ta shaida matsayin kasar na zama babbar kasa mai tasiri a duniya, tare da baiwa al'ummar Sin damar samun farfadowa da ci gaba. "

A cewar shugaban kasar Sin, "A kokarin yakar maharan sojojin kasar Japan, mutanen kasar Sin fiye da miliyan 35 sun rasa rayuka ko kuma jikkata. A sakamakon wannan babbar hasara, an samu kubutar da kasar da al'ummarta daga harin da aka kai musu, gami da samar da taimako ga mutanen da suke kokarin dakile sojoji 'yan Nazi a nahiyar Turai, da yankin tekun Pasific. "

Xi Jinping ya taba fada cewa, "Wasu jarumai sun ba da gudunmowa sosai ga yunkurin tabbatar da makomar al'umma mai haske. Yadda wadannan mutane suka sadaukar da rayukansu, ya kan zama wani labari mai burgewa, wanda ke rika ciyar da mu zuwa gaba. " (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China