Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Najeriya ta hallaka 'yan ta'adda 20 a wani hari ta sama
2020-08-20 10:36:38        cri
Hukumomin sojin Najeriya sun tabbatar a ranar Laraba cewa, a kalla mayakan kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci ta yammacin Afrika ISWAP su 20 aka kashe ciki har da manyan kwamandojinsu a yayin hare-hare ta jiragen sama wanda rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar.

Babbar cibiyar ta ISWAP tana yankin Bukar Meram dake jihar Borno a shiyyar arewa maso gabashin kasar, inda ya hada wasu yankunan tafkin Chadi, sanarwar da sojojin ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa an tarwatsa wajen a harin da aka kai da wasu bama-bamai.

John Enenche, kakakin sojojin Najariyar ya ce, harin da aka kai yankin Bukar Meram wanda mafaka ne ga mayakan ISWAP da wasu daga cikin shugabanninsu.

Enenche ya kara da cewa, wasu jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu da aka tura zuwa yankin sun lalata wuraren da aka shirya kai harin, lamarin da ya yi sanadiyyar lalata gidajen mayakan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China