Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya yi jawabi a kwalejin nazarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa ta Faransa
2020-08-31 14:47:52        cri

A ranar Lahadi 30 ga watan nan, wakilin majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi jawabi mai taken "Yin hadin gwiwa da nuna fahimtar juna, domin tabbatar da ci gaban dukkanin bil Adama cikin zaman lafiya" a kwalejin nazarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa ta kasar Faransa.

Maryam Yang na dauke da karin bayani…

Cikin jawabinsa, Wang Yi ya ce, cikin watanni da dama da suka gabata, cutar numfashi ta COVID-19 tana yaduwa cikin kasa da kasa. Ta kuma nuna ainihin halayen kasa da kasa, kamar Sin da Turai, da suka hada kansu wajen yaki da cutar, da wasu da suka nuna zargi da cin zarafin sauran kasashe kan wannan batu. Kuma, abin da ya fi cutar COVID-19 ba mu wahala shi ne "cutar siyasa", domin wasu kasashe na neman siyasantar da batun annobar, lamarin da ya sa, suka kasa warware matsalolin da suka fuskanta, yayin da suke bata hadin gwiwar dake tsakanin gamayyar kasa da kasa.

Wang Yi ya jaddada cewa, farfadowar kasar Sin, nufinsa shi ne samun wadatar kasa, da jin dadin zaman al'umma, da habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen duniya zuwa wani sabon matsayi. Wasu na ganin cewa, farfadowar kasar Sin yana nufin mallakar kasa da kasa, dangane da wannan tsokaci, ya kamata a ce, ba su san tarihi da al'adun kasar Sin ko kadan ba. Mutanen Sin ba su taba yin mulkin mallaka ba, mutane ne masu son zaman lafiya da lumana. Shi ya sa, kasar Sin ke yin kira ga kasa da kasa, don karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama.

Bayan Sin ta fara bude kofa ga waje, ya zuwa yanzu, shekaru sama da 40 sun riga sun gabata, cikin wadannan shekaru, al'ummominta sun cimma nasarori da dama bisa tsarin gurguzu na musamman da kasar Sin take bi. Karfin kasar na ci gaba da karuwa, a sa'i daya kuma, ana ci gaba da kyautata zaman al'umma. Bunkasuwar kasar Sin yana tallafawa al'ummomin kasar, yayin da yake kawo alheri ga mutanen kasa da kasa.

Ya kuma kara da cewa, domin fuskantar sauye-sauyen yanayin kasashen duniya, kasar Sin ta fidda sabon tsarin neman ci gaba, watau raya manyan kasuwannin kasar domin karfafa musayar ciniki a tsakanin sassan kasar Sin, da kuma tsakanin kasa da kasa.

Sin za ta habaka bukatun jama'a, yayin da take kara bude kofa ga waje, domin samar da damammaki ga kasa da kasa, ta yadda za ta samu farfadowa da ci gaban kanta, yayin da take ba da taimako ga kasa da kasa wajen samun farfadowa da ci gaba.

Bugu da kari, ya ce, gabanin sauye-sauyen yanayi cikin kasa da kasa, da matsalar yaduwar annoba, ana fuskantar zabi mai muhimmanci ta fuskar ci gaba ko ja baya, yin hadin gwiwa ko neman rabuwa, bude kofa ko rufe kofa. Ya ce ya dace kasar Sin da kasashen Turai su mai da hankali kan bukatun al'ummominsu, kin wadanda suke hura wutar kiyayya tsakanin kasa da kasa, domin tabbatar da zaman karko cikin kasashen duniya.

Da farko, ya ce, "ya kamata mu tsaya tsayin daka wajen neman ci gaba cikin zaman lafiya, da nuna kiyayya ga wadanda suke neman raba hadin gwiwar kasa da kasa. Kasar Sin ta ki wadanda suke neman hana bunkasuwar jama'ar kasar Sin, da ma al'ummomin kasa da kasa. Tana kuma son yin hadin gwiwa da kasashen Turai, domin neman bunkasuwa cikin zaman lafiya, da kuma nuna kiyayya ga matakan da za su haddasa sabani da tashe-tashen hankulan al'umma".

Na biyu, ya ce, "Muna goyon bayan musayar dake tsakanin kasa da kasa, da yin kira da a gudanar da harkokin kasa da kasa ta hanyar yin shawarwari. Kasar Sin tana daukar kasashen Turai a matsayin muhimmin bangaren inganta bunkasuwar kasa da kasa, tana son yin hadin gwiwa da kasashen Turai wajen kare tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, da kiyaye yanayin adalci na kasa da kasa".

Na uku, ya ce, "Ya kamata mu ci gaba da habaka hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, da kin kashe dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. A halin yanzu, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen duniya na ba da muhimmanci, kuma neman gurgunta dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da sauransu, yana nufin kashe dangantakar dake tsakaninsu, da damammakin bunkasuwa, da ma babbar kasuwa mai karfi. Ya kamata Sin da Turai su bi ka'idar 'yancin ciniki, domin kiyaye zaman karko na tsarin sarrafawa, da samar da kayayyaki na kasa da kasa, ta yadda za a bada gudummawa ga farfadowar kasashen duniya bayan annoba".

Na hudu kuma, ya ce, "Ya kamata mu hada kai domin fuskantar kalubaloli, Sin da Turai za su kasance abin koyi a fannin neman bunkasuwar kasashensu".

Haka kuma, ya ce, "Shekarar bana shekara ta cika shekaru 45 wajen kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasashen Turai. Kuma muhimman darussa da muka koyo daga wadannan shekaru, su ne, bangarorin biyu za su karfafa fahimtar juna a tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari cikin adalci, da cimma moriyar juna ta hanyar yin hadin gwiwa, yayin da ake warware sabaninsu ta hanyar yin shawarwari yadda ya kamata, da kuma fuskantar kalubaloli cikin hadin gwiwa ta hanyar karfafa mu'amalar dake tsakaninsu". (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China