Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yaba da kokarin firayin ministan Japan wajen kyautata huldarsu
2020-08-29 16:59:35        cri

A yau Asabar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya amsa tambayar da manema labarai suka yi masa game da firayin ministan kasar Japan Abe Shinzo wanda ya bayyana sanarwar yin murabus, inda ya ce a cikin 'yan shekarun da suka gabata, huldar dake tsakanin Sin da Japan tana gudana yadda ya kamata, haka kuma shugabannin kasashen nan biyu sun cimma ra'ayi daya kan yadda za su raya huldar dake tsakaninsu a sabon zamanin da muke ciki, a don haka kasar Sin tana mutunta kokarin da firayin ministan Japan ya yi, a sa'i daya kuma, ana masa fatan samun warka cikin sauri.

Zhao Lijian ya kara da cewa, kasarsa tana son yin kokari tare da kasar Japan bisa ka'idojin da sassan biyu suka tanada a cikin takardun siyasa guda hudu, haka kuma tana son kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangaren yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, tare kuma da ciyar da huldarsu gaba lami lafiya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China