Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin kwangilolin da aka daddale a bikin nuna fina-finan duniya na Beijing karo na 10 ya kai yuan biliyan 33
2020-08-29 16:03:11        cri

A jiya Juma'a aka shirya bikin daddale yarjejeniyoyin dake shafar kasuwar birnin Beijing na bikin nuna fina-finan duniya na Beijing karo na 10 a gidan rediyo da talibijin na birnin Beijing, inda kamfanoni 46 suka daddale kwangiloli kan manyan ayyuka 21, kana za a gudanar da sauran ayyuka 110 a kasuwar birnin na Beijing, gaba daya darajar kwangilolin da aka daddale ya kai kudin Sin yuan biliyan 33 da miliyan 89, adadin da ya karu da kaso 7 bisa dari bisa makamancin lokacin bara, kuma ya sake kai matsayin koli a tarihi.

Mataimakin zaunannen shugaban kwamitin shirya bikin nuna fina-finan duniya na Beijing karo na 10 kuma ministan yada manufofi na birnin Beijing Du Fei ya bayyana cewa, a cikin shekaru goma da suka gabata, gaba daya an daddale yarjejeniyoyi kan manyan ayyuka 302, wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan biliyan 165 da miliyan 28, lamarin da ya nuna cewa, bukukuwan nuna fina-finai da aka shirya a Beijing sun samu matukar amincewa daga masu aikin samar da fina-finai na kasashen duniya.

Yarjejeniyoyin da aka daddale sun shafi ayyuka daban daban, misali zuba jari kan samar da fina-finai, da gina sinimomi da sansanonin samar da fina-finai da shirin horas da masu samar da fina-finai matasa da sauransu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China