Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Faransa ya gana da ministan wajen Sin Wang Yi
2020-08-29 15:45:20        cri

A jiya Juma'a 28 ga wata, agogon wurin, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi ganawa da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi wanda ke ziyarar aiki a Faransa, a fadar Elysee dake birnin Paris.

Yayin ganawar ta su, da farko Wang Yi ya mika sakon da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tura ga takwaransa na Faransa. Kana Wang Yi ya bayyana cewa, sakon da shugaba Xi ya aikawa Macron ya nuna cewa, kasar Sin tana maida hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da Faransa, haka kuma tana martaba zumunta da aminci dake tsakanin shugabannin kasashen biyu, a don haka kasar Sin tana son tabbatar da muhimmin ra'ayi guda da suka cimma, tare kuma da kara zurfafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni.

Wang Yi, ya kara da cewa, nahiyar Turai tana taka babbar rawa kan ci gaban duniya, har kullum kasar Sin da kasashen Turai amimai ne dake gudanar da hadin gwiwa, ba 'yan takara ba ne, kuma ra'ayin daya da sassan biyu suka cimma ya fi sabanin dake tsakaninsu yawa, ya dace su yi kokari tare domin kare tunanin gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban a maimakon ra'ayin bangaranci, da haka za a iya kiyaye ka'idar huldar kasa da kasa mai tushe da kuma shirya tsarin tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba.

A nasa bangare, shugaba Macron ya furta cewa, kasarsa tana son ciyar da huldar dake tsakaninta da kasar Sin gaba, kuma tana son nuna goyon baya ga ra'ayin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin bangarori daban daban tare da kasar Sin, kana tana son kara karfafa cudanya da hadin gwiwa dake tsakaninta da kasar Sin wajen kiwon lafiyar jama'a da sauyin yanayi da kiyaye hallitu da batutuwan dake shafar kasashen Afirka, ban da haka za ta aiwatar da shawarar da rukunin G20 ya gabatar game da jinkirtar neman bashin da suke bin kasashen dake fama da talauci mai tsanani.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China