![]() |
|
2020-08-28 10:48:29 cri |
An dai, fitar da wannan sanarwar ce, yayin taron dandalin hadin gwiwar kafofin watsa labaran Latin Amurka na shekarar 2020, da aka bude ta kafar bidito yau Jumma'a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin taron, baki kimanin 33 daga kungiyoyi 15 daga kasashen Latin Amurka da Sin, sun yi tattaunawa mai zurfi kan yadda za su jure matsaloli da kuma yadda za su ci gaba kafada da kafada a fannin yaki da wannan annoba.
A jawabinsa na bude taron, shugaban rukunin CMG, kana babban edita Shen Haixiong, ya bayyana cewa, ya kamata kafofin watsa labarai, su kasance masu ba da rahotanni na gaskiya,maimakon yada jita-jita da haddasa tashin hankali, da neman cimma daidaito maimakon haddasa rarrabuwar kawuna, da nacewa wajen yaki da annoba ta hanyar kimiya, maimakon dora laifi kan sauran kasashe. Sannan a karshe, su kasance masu watsa rahotannin dake karfafa gwiwa, maimakon na takala.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China