![]() |
|
2020-08-28 10:28:12 cri |
Hukumar ta bayyana cikin rahoton ta na rana-rana da take fitarwa cewa, har yanzu akwai marasa lafiya 288 dake samun kulawar jami'an lafiya, ciki har da mutane 4 dake cikin matsanancin yanayi. Baki daya dai, marasa lafiya 80,091 ne aka tabbatar sun warke daga cutar, an kuma sallame su daga asibiti a jiya.
Ya zuwa jiya Alhamis, baki daya, mutane 85,013 aka tabbatar sun taba kamuwa da cutar a babban yankin kasar, daga cikin su, cutar ta halaka mutane 4,634.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China