2020-08-07 19:48:23 cri |
Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC) ta bayyana Jumma'ar nan cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a sassan nahiyar, ya zarce miliyan daya.
Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka mai mambobin kasashe 55, ta bayyana cikin rahoton ta na baya-bayan nan da take fitarwa game da yanayin cutar a sassan nahiyar cewa, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a sassan nahiyar, ya karuwa zuwa 1,007,366 ya zuwa tsakar ranar yau.
Rahoton cibiyar ya nuna cewa, yawan mutanen da suka mutu sanadiyar cutar, ya karu daga mutane 21,617 a ranar Alhamis zuwa 22,066 a yau Jumma'a.
Kasar Afirka ta kudu ce cutar ta fi yiwa illa a nahiyar, inda ya zuwa yanzu aka tabbatar da mutane 538,184 da suka kamu da cutar, sai kasashen Masar da Najeriya da Aljeriya da Morocco dake biye mata baya.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China