Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tallafawa ayyukan tsaron kasa da kasa
2020-08-18 10:57:07        cri

Babban hafsan sojojin Najeriya Janar Gabriel Olonisakin, ya ce dakarun sojin kasar za su ci gaba da shiga a dama da su a ayyukan tallafawa tsaron shiyya-shiyya da ma na kasa da kasa.

Janar Olanisakin, wanda ya bayyana hakan jiya a helkwatar tsaron kasar dake birnin Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce Najeriya na da burin samar da tallafin dakaru, da kayan aiki da ake bukata, a ayyukan wanzar da zaman lafiya dake wakana a sassan nahiyar, da ma ragowar yankunan duniya. Za ta kuma ci gaba da kare matsayinta na mai ba da gudummawar wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.

Olonisakin ya kara da cewa, a baya bayan nan gudummawar da Najeriya ke bayarwa a wadannan fannoni ta ragu, sakamakon wasu dalilai. To sai dai kuma ana daukar matakan zaburar da matsayin kasar, ta yadda za ta fadada gudummawarta a irin wadannan ayyuka, da ma hadin gwiwar da take yi tare da sauran abokan hulda na sauran sassan duniya, duka dai da nufin wanzar da zaman lafiya da tsaro, a daukacin sassan duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China