2020-08-20 09:40:25 cri |
Shugaban hukumar lura da 'yan ci rani ta kasa da kasa ko IOM dake aiki a kasar Libya Mr. Federico Soda, ya ce wasu 'yan ci rani su kimanin 45 sun rasa rayukan su, bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya nutse a gabar tekun kasar Libya.
Jami'in wanda ya wallafa sakon tabbatar da aukuwar lamari a shafin sa na twita, ya ce wannan ne karon farko da aka samu rasuwar 'yan ci rani mafi yawa a lokaci guda a shekarar bana. Kuma babu wani shiri na musamman karkashin kungiyar tarayyar Turai ta EU, da aka tanada domin bincike da ceton mutanen.
Tun bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi a shekarar 2011, kasar ta tsunduma cikin yanayi na runadi da tashe tashen hankula, lamarin da ya bude kofar kwararar dubban bakin haure dake shiga kasar da nufin tsallakawa kasashen Turai ta barauniyar hanya ta tekun Meditireniya.
Alkaluman hukumar IOM sun tabbatar da cewa, a shekarar nan ta 2020 kadai, an yi nasarar ceto sama da 'yan ci rani 7,000 daga tekun Libya, wadanda ke shiga kasar ba bisa ka'ida ba da nufin ketarawa kasashen Turai. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China