Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya halarci taron kwamitin sulhun MDD kan batun Libya
2020-07-09 10:14:21        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi a ranar Laraba ya halarci babban taron kwamitin sulhun MDD ta kafar bidiyo game da batutuwan dake shafar kasar Libya da gabatar da wasu muhimman shawarwari hudu a madadin gwamnatin Sin wadanda za su taimaka wa kasar Libya wajen komawa turbar zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin hanzari.

Na farko, tsakaita bude wuta da dakatar da tashin hankali. Wang ya ce, kasar Sin ta bukaci dukkan bangarorin Libya da su gaggauta tsakaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, kana ta bukaci dukkan kasashen da abin ya shafa da su yi kyakkyawan aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD.

Na biyu, a yi amfani da matakan siyasa wajen warware sabani, wanda shi ne kadai hanya mafi dacewa don warware rikicin kasar Libya, Wang, ya kara da cewa, kasar Sin ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su koma kan teburin sulhu.

Na uku, a yi kokarin kawar da dukkan abubuwan dake janyo rikicin Libya domin kare kasar daga zama wata cibiyar yaduwar ayyukan ta'addanci.

Na hudu, mutunta ka'idojin MDD.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China